Image default
Computer Tutorials

Yadda Ake Connecting Din Xender da computer a tura files cikin Sauki

Assalamu Alaikum barkan mu da wannan lokaci, sannun mu kuma da sake saduwa daku a wannan lokaci.

To kamar yadda aka sani muna kawo abubuwan da suka dan ganci Computer da Android a wannan shafi mai Albarka wato Arewa Fikira Tech.

To yau insha Allah zamuyi bayani ne akan yadda ake tura file ko kuma wani abu da ya danganci turawa daga android zuwa computer din ka, ko kuma daga ita computer din zuwa Android, ta hanyar connection da xander application.

Ba wani abu bane mai wahala a wannan post din insha Allahu zamu yi bayani duka akan steps din da ake bi don ayi connecting din xender application da computer ta hanyar amfani da hotspots.

Yin transfer daga wayarka zuwa computer din ka ko kuma daga computer zuwa wayar ka yana da amfani musamman ma idan mutum bai da USB cable ko kuma wurin ya lalace a computer din sa to insha Allah wannan hanyar zata taimaka sosai da yardar ubangiji.

Dan haka yanzu zamuyi amfani da fasahar wireless connection wato Wifi da hotspots a tsakanin wayar ka da computer din ka, amma computer din ka ta kasance tana da hotspot driver.

To da farko dai bayan ka tabbatar kana da manhajjar hotspots driver, sai kuma ka tabbatar kanada manhajjar Xender a wayarka in baka da ita sai kaje manhajjar Playstore kayo Downloading, bayan kasauke ta kayi install nata a wayarka sai kuma kaje Computer din ka kasauke manhajjar Browser irin su Chrome, Firefox, Opera Uc-browser , da dai sauran duk wasu manhajja da ake browsing dasu ka tabbatar kanada guda daya a cikin su akan Computer naka.

To idan ka tattara wadannan abubuwa shikenan sai kabi steps din dazamu kawo a yanzu, ko nace kabi matakan da zamu ambata a post din nan a yanzu Insha Allahu.

Mataki na Daya:-

Za ka/ki shiga xender a cikin android din ka

Mataki na biyu:Zaka danna daga sama gefen dama na Xender naka zakaga wasu dugo-dugo guda uku saika tabasu, idan katabasu zasu bude kamar haka yadda kake gani saika taba inda aka rubuta Connect to PC

kana taba Connect to Pc zai baka wanna wajen kamar haka:-

Kana ganin haka saika taba inda akasa Hotspot kana tabawa zai kawoka wajen da zaka bude hotspot na wayarka sai ka kunnashi, kana kunnashi sai kayo back zai dawo dakai wannan wajen kamar haka:-

Daga kasa ka kalla zakaga wasu Lambobi da suke nuna IP-adress naka Kana ganin wadannan lambobin sun fito, to kawai ka Kalli Computer naka zakaga ta nuna Abin Service yafuto a cikin ta to kawai kana ganin abin service din yafito zakaga Connect saika taba Connect din kana taba Connect din, sai kazo ka shiga cikin browser ta computer din ka, sai ka rubuta ip address din da xender ta nuna maka a can saman inda Ake rubuta website address a Chrome din computer din naka zaka rubuta kamar Haka :-

To da kayi wannan shikenan idan ka zabi photo ka danna alamun download a cikin computer zakaga ya sauka a ciki, idan upload ka danna zaka ganshi a wayarka.

Idan ka sauko ko kuma ka tura daga wayar ka zuwa computer to a computer zaka duba folder wadda ake cema Downloads nan zaka samu abubuwan da ka turo.

To Alhamdulillah wannan itace hanya mafi inganci da muka yadda da’ita wajen tura abu daga Xender na waya zuwa cikin wayar daga Computer, ko kuma muce daga waya zuwa computer, ko kuma muce daga Computer zuwa cikin waya duka daya ne.

Mai tambaya ko Karin bayani yana iya yi mana comment domin mu duba mubashi amsa Insha Allah.

Kuci gaba da kasancewa da Arewa Fikira Tech domin karuwa da abubuwan da suka shafi Technology na waya da computers,da dai sauran su.

Sannan kada ku manta wajen tura duk wani post namu da kuka karanta zuwa social medias domin ‘yan uwa sugani suma su Amfana.

Sannan ku gayyato mana abokan ku domin su ziyarci wannan website namu mai Albarka domin karuwa da abubuwa da dama a wannan website Mungode da kasancewa damu da kukayi a wannan lokaci Mai Albarka.

AREWA FIKIRA TECH

Ke muku fatan Alkhairy akodayaushe

Leave a Comment