
Assalamu Alaikum ‘yan uwa barkanmu da wannnan lokaci sannu mu kuma da sake saduwa daku a wannan lokaci.
To yauma kamar kullum gamu dauke da wani darasi wanda zai matukar taimaka muku a wayoyin ku na Android, mussamman ga wadanda wayoyin su suke daukar zafi ko kuma suke kamewa.
To wannan hanyar zata zaimaka muku sosai da sosai wajen hana wayar taku kamewa da kuma yawan yin zafi.
Bakomai bane yakansa waya tana kamewa ko tana yawan daukar zafi illah Lodi da kukewa wayoyin naku da har zaizo yafi karfin nauyin ram din da wayar taku tazo dashi, wanda hakan ka ‘iya jawowa kamewar waya ko kuma sakata yin zafi.
Indai wayarka kaga tana yawan kamewa ko daukar zafi matukar ba ram din tane ya cika ba ko kuma injin wayarka yafara samun matsala ba, to tabbas Notification da yake shigowa wayarka yanawa wayar taka nauyi sosai, to hakan zaisa tana kamewa ko daukar zafi.
To yaza’ayi ka rage yawan shigowar Notification din wayarka ko kuma ka dakatar dashi ma gaba daya dan wayarka ta rinka samun sukuni a duk lokacin daka bude data.
To yau darasin da zamuyi kenan dan haka saiku biyomu dallah-dallah domin jin yadda ake hana Notification shigowa waya gaba daya.
To dafarko idan kazo kan wayarka kafin ka kunna Data, zaka janyo Notification na wayarka saika tsaya ka nutsu a cikin wadannan Notification din na wayarka zakaga wani waje an rubuta Do not disturb 🚫 , to zaka ganshi a kashe kawai saika kunnashi kamar yadda kake gani a wannan hotan kamar haka:-

Amfanin wannan Do not disturb 🚫 din shine, Koda Notification sun shigo wayarka bazai bari su takurawa wayarka ba, zai na boye duk wani Notification dazai shigo wayarka ya takurawa wayar ka, kuma zai hana wayarka yin zafi sanadiyyar ya boye notification da suke shigowa suke addabar wayarka har ta rinka yin zafi, dan haka shi Do not disturb 🚫, bawai yana Hana Notification shigowa bane yanadai boyesu matukar ka kunnashi, amma da zarar Notification sun gama shigowa wayarka idan kazo ka kasheshi zakaga duka notification din ka suna nan, dan zai sauke masu duka kuma lokaci guda sabanin da idan ka kunna Data zasu na ta zuwa da dai-dai da dai-dai har su hanaka sakewa da baka dama wajen shiga duk inda kakeso a wayarka har sai kajira wannan Notification din sun gama zuwa to Amfani do not disturb kenan a wayoyin na Android da suke zuwa dashi da wasu basusan amfanin sa ba.
Note A kula
Akwai wayoyin da basa zuwa da Do not disturb 🚫, to wadannan suyi hakuri zamu kawo musu rubutu da kuma video na yadda zasu hana duk wani application dazai na sauke musu Notification yana takura musu.
Fatan kunji dadin wanna video kuma zakuje ku gwada amfani da wannan hanyar da muka kawo muku dazata taimaka muku wajen hana wayarku kamewa da daukar zafi
kada kumanta kuna tare da website na
Arewa Fikira Tech
Kuna share a social medias na duk rubutun da kuka karanta kuka amfana dashi a wannan website mai Albarka dan ‘yan uwa suma su shigo su karanta su amfana.
DOMIN GANIN CIKAKKEN VIDEON
MUNGODE 👍

