Image default
Adsense for YouTube

Menene Adsense Kuma Yaya Ake Budeshi

Assalamu alaikum, Barkan mu da sake kasancewa a wannan shafi namu mai albarka mai suna AREWA FIKIRA.

A yau Insha Allah zamu yi bayani ne akan Adsense da kuma yadda zaka bude shi kayi amfani dashi a channel din ka ko kuma a website din ka.

DA FARI DAI MENE NE ADSENSE?

Adsense wani bangare ne ko kuma ince wani reshe ne daga rassan kamfanin google kamar yadda dai YouTube yake reshe daga kamfanin google, wanda kamfanin na google suke amfani dashi wajan tallatawa kamfanunuwan duniya da manyan manhajoji ko platforms hajojin su ga al’ummar duniya, ma’ana ga mitane masu bibiyar shafuka da kuma manhajojin kafanin google, kama daga manhajar YouTube, da kuma website da mutane ke kirkira a Google din kansa dama sauran manhajoji da kuma applications ko kuma games ko manyan shafukan yada labarai da al’amuran yau da kullum ko wasu ilmi da mutane ke iya bincike akan sa.

Kamfanin na Google adsense suna karbar tallace tallacen kamfanunuwa sannan su saka a shafukan masu kirkira ko YouTube channel na masu kirkira wato CREATORS wanda ta silar kallon wannan tallar ne masu kirkirar ayyuka a shafuka da kuma tashoshin YouTube din ke samun kudi daga shi kamfanin na adsense idan kayi join dasu bayan ka cika duka sharrudan su da suka gindaya maka.

Ana mutukar samun alheri sosai ta hanyar Adsense a bangarori kamar haka.

1.YOUTUBE

2.WEBSITES

3.APPLICATIONS

4.GAMES DA DAI SAURAN SU.

Saboda haka zaka iya kirkirar daya daga cikin wadannan abubuwa domin fara gabatar da abin da kake ganin zaka iya farawa domin fara samun naka kason a wannan tsari na adsense.

YAYA AKE BUDE ADSENSE?

Yadda ake bude Adsense account abu ne mai matukar sauki wanda ina ganin baza ka bata sama da minti biyar ko goma ba wajan kirkirar sa ba.

Saboda da haka idan kana bukatar koyon yadda zaka bude din to danna wannan rubutun da aka rubuta “WATCH VIDEO HERE”.

Mungode da ziyartar wannan shafi namu mai suna AREWA FIKIRA.

Leave a Comment