
Barka ka da zuwa wannan shafi namu mai suna Arewa Fikira.
A rubutun mu na yau a cikin wannan shafi namu mai albarka mun kawo muku bayani akan yadda zaka rufe subscribe din channel din ka yadda babu wanda zai ke gani sai kai kadai.
Da fari kana bukatar manhajar chrome domin yin wannan abu, idan ka mallaki manhajar chrome sai ka shiga cikin ta daga nan sai ka shiga shafin YouTube kamar haka 👉www.youtube.com👈 bayan ka shiga ya bude maka zaka ga wasu yan alamar digo-digo guda uku daga bangaren hannun ka na dama

sai kayi click akan sa in da zai nuna maka jadawalin rubutu masu yawa amma a ciki zaka ga gunda aka rubuta (desktop site)

kana dannawa zai bude maka fuskar YouTube studio din sai kuma ka danna kan logon channel din ka dake bangaren hannun ka na dama.

shima zai sake bude maka wasu jadawalin rubutu masu yawa sai ka zabi in da aka rubuta YouTube studio sannan kayi click akai.

bayan kayi click zai sauya izuwa wata subuwar fuskar studio din, sai ka duba can kasan YouTube studio din zaka ga wata yar alamar setting yar karama daga can kasa

Sai kawai kayi click akan ta zaka ga ta bude maka wata yar akwati mai square sannan zaka ga wani guri an rubuta (channel)

Sai ka danna akan sa in da a cikin sa zaka ga jerin rubutu sai ka danna akan inda aka rubuta (Advance setting) sai kayi kasa zaka ga wani guri da aka rubuta (Display the number of people subscribe to my channel) sai kayi click akai zaka ga tick din nan ya bace sai ka danna save daga shikenan ka boye subscribe din channel yadda babu wanda zai gani sai kai kadai.

Zaka iya kallon cikakken video akan yadda ake yin abin dalla dallah.


