
Assalamu Alaikum barkan mu da wannan lokaci sannun mu kuma da sake saduwa daku a wannan darasi namu mai Albarka.
kamar yadda muke tashan tambayoyi akan website kama daga kan yadda mutum zai fara creating na website har yayi masa design ya fara posting da yadda zaina samun views a website din nasa har zuwa lokacin dazai sawa website din nasa Adsense har yafara samun kudi.
munashan tambayoyi da suka danganci hakan, wanda duka babu wanda bamuda amsar sa saidai rashin lokaci dazai sa mukasa baku amsar.
Amma cikin hukuncin ubangiji insha Allah a bisa kokarin da mukeyi dan ganin mun fara kawo muku rubutu akan website din gaba dayansa, da yadda zaku kirkireshi, da yadda zaku na samun visitors, da yadda zakuyi masa design yayi kyau, da yadda zata kaiku harku nemi Adsense kufara samun kudi.
To yanzu mun yanke shawarar zamuna kawo muku rubutu akan website din duk ranar juma’ah insha Allah.
Domin muna ganin ta hakane zamu sami damar amsa duka tambayoyinku da suka shafi website da Adsense din kansa.
Dan haka muna kira ga duk kanin masu ziyartar website namu da suna ziyartar bangaren Website for Adsense duk ranar juma’ah domin suna samun rubutukan mu akan website, domin sanin yadda zaku kirkiri website da yadda zakuyi masa design da samun kudi.
Amma akarshe ina kira ga dukkanin maziyartan wannan website mai Albarka da duk wanda yashiga ya karanta post namu akan website da yadaure ya ringayin share na Posting namu domin ‘yan uwa su shigo sugani suma su amfana.
Akarshe muna godiya ga dukkannin visitors namu Allah yabarmu tare.
AREWA FIKIRA TECH

