Image default

Youtubers da dama na yawaita tambaya akan cewar “shin zaka iya ka sake dora videon da da can ka taba dora shi a channel din ka, kuma idan kayi hakan shin ba zai jazawa channel din taka wata matsalar ba?”

Dangane da wannan tambaya dai to insha Allah ga amsar ku.

Da fari dai abin lura a nan da ya kamata ka fara la’akari dashi shine, akwai wani abu da kamfanin YouTube suke kira “VIDEO ID” wanda wannan abu mai suna VIDEO ID da shine kamfanin YouTube suke amfani wajan gane kowanne video da aka dora a manhajar su ta YouTube. kuma da shine suke gane cewar wani yayi amfani da videon channel din wani imma ya kasance ya nemi izinin sa ko kuma akasin haka.

Saboda haka ne ma kamfanin na YouTube suka fitar da doka ko kuma ince sanarwa akan cewar basu yadda wani yayi amfani da videon channel din wani ba ba tare da yayi wasu sauye sauye ba. Ma’ana in dai kana bukatar yin amfani da videon wani to dole sai ka sauya wani bangare na bidiyon kafin ka dora a channel din taka saboda ta hakan ne za’a samu banbanci na VIDEO ID din tsakanin channel din taka da kuma tasa. Kuma ta haka ne YouTube zasu iya banbancewa masu neman wannan bidiyo channel din da ya kama ta su samu videon.

Saboda haka dangane da sake dora videon da ka taba dorawa a channel din ka baya ma dole ne sai dai ka sakewa videon fasali kafin ka sake dorawa a channel din taka, saboda ta hakan ne YouTube zasu yadda da videon da ka dora a channel din taka.

Idan ka dora video wanda ka taba dorashi a baya to kafin videon ya kammala uploading YouTube zasu ce maka “you have already uploaded this video” ma’ana suna fada cewar ai ka riga da ka dora videon tun ba yanzu ba, saboda haka idan zaka dora shi sau dubu to asarar datar ka kawai zaka yi ta yi, saboda YouTube baza su bari videon ya hau kan channel din ba baya da cewar dama an taba dora shi a baya.

Da fatan kun gamsu tare da fahimtar duka bayanan mu akan wannan matsalar da kuma yadda zaku kiyaye ta.

Domin kallon videos masu muhimmanci akan YouTube to ka shiga wannan link din dake kasa in da aka rubuta “Kasuwar YouTube”👇👇👇👇👇

Leave a Comment