
kamar yadda kuka sani ofishin hakkin mallaka na N-Power wato National Social Investment Management System, sun bawa dukkan wanda yasamu N-power a karo na biyu damar zuwa ayi masa Verification na daga tomprint har zuwa dora takaddunsa da zasu nuna shaidar cewa shine mai wannan bayanan dake kan Dashboard dinsa na N-Power.
Saboda wannan Verification da ake tayi ga duk wanda yasamu ‘yan power a karo na biyu yasa wasu wadanda they are under Non-Graduate, ma’ana wadanda suka nemi N-power da Secondary school kenan, kamar irin wadanda suka cike N-power da
N-Tech
N-Creative da kuma
N-Build suke daukar takaddunsu suke zuwa ayi musu verification wanda a karshe sai dai a karo su akiyi musu verification din ko menene Dalili⦅…..
To ofishin N-power wato
National Social Investment Management System, ya fitar da sanarwar cewar wanna Verification din da akeyi badda wadanda suka cike N-power da Secondary school ma’ana Non-graduate badda su a wannan Verification din dan haka su daina wahalar da kansu wajen zuwa verification suna sanar da cewa duk wanda ya cike N-power da Secondary school kuma yasan ya cike daya daga cikin wadannan:-
N-Tech
N-Build
N-Creative
To ana sanar dasu cewa da kada su kara zuwa wajen verification za’azo ayi musu nasu verification din daga baya a wajajen da za’a turasu training wannan fadar ofishin ce, inda yanzu haka zan nuna muku rubutun da sukayi akan hakan:-

wannan shine gaskiyar magana a takaice kan Non-Graduate da suke kokarin zuwa verification na N-Power ina fata zakuyi hakuri har zuwa lokacin da za’azo ayi muku naku.
Muma muna muku fatan Alkhairy, Allah ubangiji ya baku sa’ah Amin.
AREWA FIKIRA TECH

