Image default
Apps Tutorials

Yadda Zaka yi Zanen Hotan ka a Wayar ka Cikin Sauki

Assalamu Alaikum maziyartan wannan website namu mai Albarka kamar yadda nace yau insha Allahu zan mana bayani akan yadda mutum zaiyi zanen hotansa a wayarsa ta hanya mai sauki tamkar yadda muka zana namun nan yayi kyau sosai to insha Allah yau zan koya mana yadda zakuyi kuma ku hada naku da kanku ba kuda matsala insha Allahu.

To abin babu wahala a gurguje muyi abinda yakawo mu.

ABU NA FARKO (1)

Zaka Shiga nan kadauko Application din

Bayan ka daukoshi ABU NA BIYU (2)

Saika budeshi, bayan ka budeshi zai nunoma wannan fuskar kamar haka:-

Bayan ya nunoma wannan fuskar kamar haka,anan zaka zabi kalar fuskar, ko kuma ince kalar zanen da kakeso fuskar taka takasance, zakaga kalar fuskoki daban-daban birjik dayawa kawai saika zabi kalar wacce kaga tama kashiga, kana shiga zai nunoma wannan wajen kamar haka:-

Yana nunoma nan idan kakula daga kasan hotan zakaga hotan alamar Camera da Gallery, to kawai saika shiga mai hotan alamar Gallery din, kana shiga zai kai ka kan gallery din ka kokuma folders na wayarka dan dauko wa hotan da kakeso kasa din, saika dauko hotan da ka keson sawa din, kana daukowa zakaga yafara processing kamar haka:-

Saika dan jira yagama precessing din yana gamawa zakaga hotanka ya canzu, kamar yadda kuke gani yanzu hotan mu wanda mukasa yake processing ya canzu zuwa wannan gashi nan kamar haka:-

To kawai kana ganin haka shikenan hotan ka yagama zanuwa ba kada matsala insha Allahu, kawai yanzu saura saving ma’ana yadda zakayi saving din hotan ya sauka akan wayarka.

Yadda zakayi Saving din kwa shine, daga saman hotan za kaga wata ‘yar alama kamar ta share kawai saika danna ta, kana dannawa sai ka duba daga kasa za kaga wani waje ansa Download saika danna shi, shikenan hotan ka zaiyi download ya zauna akan wayar ka ko kan memory naka ma’ana dai kan Gallery naka kamar yadda kuke gani yanzu haka nawa yayi Save ya sauka cikin gallery na:-

Shikenan kagama zanen hotanka ba kada matsala dan’uwa.

                            NOTE

Kada kamanta Dan’uwa wajen ajiye mana commen naka idan darasin namu ya birgeka.!!

Sannan kada a manta wajen yin share din post din dan ‘yan uwa su shigo sugani suma su amfana.

AREWA FIKIRA TECH

         

Related posts

Yadda Zaka Dauko Sabuwar KineMaster Ta Kyauta 2022-2023

ArewaFikira

Yadda Zaka Gano Original Plastic National Id-Card din ka Har kadauko kayan ka kana Amfani Dashi “New update)2022

ArewaFikira

Leave a Comment