Image default
Apps Tutorials

Yadda Zaka Dauko Sabuwar KineMaster Ta Kyauta 2022-2023

Maraba da zuwa wannan shafi namu mai suna AREWA FIKIRA.

A bayanin mu na yau zamu kawo muku bayani ne akan sabuwar kinemaster app ta shekarar 2022 zuwa 2023 wadda ta kyauta ce kuma baka bukatar siyan komai a cikin ta da kudi kamar yadda zaka siya a wacce zaka dauko a playstore, wanda sanin kan ku ne cewar kinemaster ta playstore tana da wasu matsaloli guda biyu da zasu sa kaji baka son ta kuma baka son yin amfani da ita, musamman ma mu anan kasashen africa kuma african ma musamman yankin Nigeria, Niger da dai sauran kasashe da suke fama da kansu ta fuskar rayuwar yau da gobe.

Matsala ta farko da kinemaster ta playstore take da itace kamar haka, Tana da abin da ake kira (watermark) wanda watermark wani abu ne da yake takurawa duk wani mai son amfani da ita ko kuma ince mai amfani da manhajar ta kinemaster.

Watermark shine wannan dan logon da kinemaster take rubutawa daga saman ta wanda ba zasu cire maka shi ba sai ka biya kudi, wanda kuma idan ka biya din ma akwai adadin lokacin da zasu baka wanda idan ya kare dole sai ka sake siya, idan ba haka ba ya dawo ya cigaba da bayyana wanda duk wanda yake amfani da KINEMASTER nasan baya son wannan abu.

Sai matsala ta biyu wadda itace duk wasu effect masu amfani kama daga music effects, video affect, ko layers effects da suke ciki baka da damar kayi amfani da su sai ka siya, ma’ana sai ka biya kudi, kuma dai shima akwai kayyadajjen lokacin da suke karewa dole sai ka sabunta siya duk wata ko sati ko kuma shekara.

Saboda haka ne muka ga ya kamata mu kawo muku wannan bayani akan yadda zaka dauko ta kyautar ta cikin sauki ba tare da ka sha wata wahala sosai ba.

Saboda idan kana da bukata zaka iya biyo bayanin yadda zaka dauko ta cikin sauki amma kafin nan muna so ka sani dole sai ka dauko wacce girman ta yazo dai dai da girman wayar ka saboda kada ka dauko wacce ba zata yi a wayar ka ba.

saboda haka a cikin jerin link din da zamu bayar dole ne ka zabi wanda zai yi a wayar ka saboda haka idan ka san wayar ka bata wuce daga version 4 zuwa shida ba sai ka dauko link na farko idan kuma kasan wayar ka ta haura daga version 6 zuwa 8 ko 10 zuwa sama zaka iya amfani daga link na biyu zuwa link na karshe.

Domin dauko su ga link din su nan a kasa.

Related posts

Yadda Zaka yi Zanen Hotan ka a Wayar ka Cikin Sauki

ArewaFikira

Yadda Zaka Gano Original Plastic National Id-Card din ka Har kadauko kayan ka kana Amfani Dashi “New update)2022

ArewaFikira

Leave a Comment