
Assalamu alaikum, barkan mu da sake kasancewa a wannan shafi namu mai albarka mai suna Arewa Fikira tech, wanda a yau mun zo muku da gabatarwa akan tsarin YOUTUBE FOR CREATORS, tsarin da zai taimakawa duk wanda yake da sha’awar fara harkar YouTube tun daga tushe har zuwa lokacin da zaka kai matakin da zaka fara samun kudi a YouTube
A cikin wannan tsari zaku koyi yadda zaku fara harkar YouTube tun daga tushen yadda zaka bude channel da kuma nau’o’in abubuwan da zaka iya kirkira ka dora a channel din ka ka kuma fara samun samun kudin dashi.
Wadannan sune jerin abubuwan da zaka iya koya har izuwa matakin kwarewa a cikin wannan tsarin namu mai suna AREWA FIKIRA.
1.Bude YouTube channel
2.Verify na YouTube channel
3.Yadda zaka saita komai na channel din
4.Irin ayyukan da zaka dora a channel din ka
5.Yadda zaka fara dora ayyuka a channel din ka
6.Yadda zaka samu subscribers cikin sauki
7.Yadda zaka samu views cikin sauki
8.Yadda zaka shahara a YouTube kowa ya sanka
9.Yadda zaka yi apply a YouTube
Da dai sauran abubuwan da ba zasu lissafu ba a gabatarwa.
Saboda haka idan kana bukatar ka fara harkar YouTube kuma kasan yadda zaka cimma bukatar ka a YouTube ka fara samun kudi sai ka danna wannan link din dake kasa domin ziyartar channel din mu wadda a cikin ta zamu koyar da komai insha Allah.

