DALILAN DA YASA AKE KWACE ACCOUNT DA KUMA SHAWARWARI DA ZAKABI NA YADDA BA WANDA ZAI KWACEMA ACCOUNT DINKA DUK GIRMAN IYA KUTSEN SA.

Tabbas a wannan zamanin da muke ciki akwai hanyoyi da masu kutse suke bi wajen kwatowa bayanan mutum batareda yasani ba, hasalima sai kaga bakai kabasu bayanan kaba amma sun samo bayanan naka wanda akarshe sai kaga sun kwace bayanan ka batare daka ankara ba, hakan tasa kanaji kana gani zaka hakura da account din naka ko kuma abinda suka kwacema din
KUMA ABINDA BAKA SANI BA SHINE
Idan aka kwace account dinka ba kai kadai matsalar za ta shafa ba, idan kai ba ka damu da kanka ba to kayi tunanin wasu da matsalar za ta shafa. Sanin kanmu ne cewa kwanakin nan an faye yawan datse accounts na mutane musamman na Facebook, har da a susunsu na banki, to muyi hattara ‘Yan uwa!!
Ga shawarwari guda biyar kacal idan za ka iya binsu sai Allah ya tseratar da mu baki daya.
1. Ka da rika amfani da password mai sauki, kayi amfani da “strong password” kamar yadda masana suka umarta. Ka da ka sa date of birth, lambar waya ko wani sunanka ko sunan budurwarka. Akwai dalili mai karfi da ya saka masana sukace hakan, wanda idan mukace zamu fadi dalilan yanzu anan zaku kosa da karantawa batare da kuma munkai fadin dalilan duka ba, kai dai ka kiyaye kawai.
Misali na “Strong Password”
Shine kamar haka za kana kirkirar Password din ka a duk lokacin daka tashi kirkirar sa
“AuK&i)all(JiG%20+20*jp.J&a”
2. Ka da ka ajiye lambar wayar da aka sanka da ita a matsayin phone number ka da ka saita account naka da ita. Idan son samu ne ka da ka bari wani ya taba sanin lambar ma balle kayi rajista da ita a wani wuri.
3. Ka da ka kasance mai amfani da password daya a ko ina, misali password dinka na Facebook ya kasance daban da na Instagram, Gmail, da dai sauran su, sannan ka daina yawan rajista da websites ko apps din da ba ka san sahihancinsu ba, kuma kayi hattara da bin links din da baka yadda dashi ba!!
4. Ka saita two-factor authentication, da logging notification, sannan kayi verifying identity naka.
5. Ka da ka sake ka ba wa wani details naka, kuma kayi hankali da email naka sosai.
Wadannan sune dalilai guda biyar da nake ganin idan mun bisu insha Allah masu kwacemana account zasu na shan wahala kafin su gano bayanan mu, kai hasalima a karshe zan iya cewa sai dai su hakura su kyale account namu domin basu isa ganowa bayanan mu ba duk girman iya kutsen su.
Kaje ka gayyato abokan ka da ‘yan uwanka domin suma suzo su karanta wannan post din sukaru su kuma karu da wasu muhimmman abubuwan a wannan website din mai Albarka.
Allah ya tsare mu baki daya Ameen!!!
SHAWARWARI DAGA AREWA FIKIRA TECH

